Wani kwararre a harkar aikin gona tare da Cibiyar Noma ta Kasa da Kasa (IITA) dake Ibadan ta Jihar Oyo, Mista John Obaniyi, ya ce idan Nijeriya tana son shawo kan dimbin kalubalen da take fuskanta, dole ne ta koma aikin gona ka’in da na’in.
Obaniyi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana kan taro mai taken ‘Dabarun kasuwanci a Harkar noma’ ga membobin masu hidimar kasa na ‘2021 Batch’ B ‘Stream II’ a sansanin NYSC dake Ikare Akoko ta Jihar Ondo.
Ya ce idan Nijeriya tana son ta zama koriyar kasa a rika yi mata hassada to dole ne ta koma harkar noma wanda a cewarsa fasaha ya kawo sauki.
“Ayyukan da aka biya ko saka hannun jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙi yana da fa’ida amma idan da gaske kuna son kasancewa a saman kuma ku kasance masu dacewa, kowane sashi a duniyar aikin gona shi ne mafi kyawun wurin zama.
Obaniyi ya ce matasan da suka kammala karatu da aka shirya domin yi wa kasa hidima suna da abin da ake bukata domin kawo sauyi a fannin aikin gona don samun ingantaccen tsarin tattalin arziki.