Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce noma na iya zama muhimmiyar gudummawa ga asusun gwamnatin tarayya, duba da yadda ake fuskantar karancin kudaden shiga, musamman a jihohin kasarnan.
Farfesa Osibanjo ya bayyana haka ne yau Talata a lokacin da yake zantawa da wata tawaga daga Hukumar Raya Muradun Yamma (DAWN), wacce ta kai ziyarar ban girma a fadar shugaban kasa wato Villa, dake birnin Abuja.
Mataimakin shugaban kasar ya ce abin da ake bukata domin bunkasa aikin samar da albarkatu shi ne jajircewa da kwazo da duk masu ruwa da tsaki a fannin.
Farfesa Osinbajo, wanda ya yi magana bayan ya saurari wani bayani kan tsarin hukumar na samar da sauyi mai dorewa a jihohi, ya ce, “noma na iya zama mafita ga dimbin bukatunmu Najeriya, da dimbin bukatun kasar na albarkatu.
A yayin da yake yin tsokaci kan abubuwan da aka samu a shekarun 1950 da 60 a fannin noma a gwamnatocin yankin na wancan lokacin, ya ce, “Gaskiyar lamarin shine, bambancin da ke tsakanin wancan lokaci da yanzu shi ne son zuciya. Babu tambaya ko kaɗan cewa akwai ƙarin bayani a yau fiye da yadda ake da su a lokacin amma dole ne wani ya kasance yana da niyyar yin hakan.
“Babu shakka ko kadan, kowane sashe na Najeriya, idan akwai isashen sadaukarwa da aiki tukuru, zai iya ciyar da kasa baki daya. Akwai kananan kasashe da ba su kai girman Jiha daya a Najeriya ba da suke samar da isassun kayan amfanin gona da fitar da su zuwa wasu sassan duniya.”
Osinbajo, wanda ya kuma bayyana mahimmancin hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu wajen kawo sauyi a harkar noma, ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su mai da hankali kan bincike da ci gaba.
Tun da farko a nasa jawabin, Darakta Janar na DAWN, Mista Seye Oyeleye, ya yi wa mataimakin shugaban kasar bayanin irin kokarin da aka yi tsawon shekaru, inda ya bayyana cewa hukumar ta samar da tsare-tsare na ci gaban fannin kiwon lafiya da ilimi a jihohi shida na Kudu da Yamma.
Ya kuma bayar da misali da farfado da noman koko da tsarin samar da dauwamammen sauyi a fannin noma a yankin, daga cikin nasarorin da hukumar ta samu cikin shekaru tara da kafa ta.