An fara gasar kwallon kafa ta mata ta 2019 wadda hukumar FIFA ke shiryawa. Wannan ne karo na takwas da ake gudanar da wannan gasar da ake yin ta a kowace shekara hudu.
A bana za a gudanar da gasar daga 7 ga wannan watan zuwa 7 ga watan Yulin a Faransa. A wasan farko da aka yi a daren jiya, Faransa ta doke Koriya ta Kudu da ci 4 da nema.
Ita ma kungiyar wasan kwallon kafa ta mata daga Najeriya, Super Falcons ta yi wasanta na farko, inda ta kara da kasar Norway, kuma an tashi wasan Norway ta doke Najeriya 3 da nema.
Wadanda suka kalli wasan sun ce abin bai musu dadi ba, amma duk da haka ba su karaya ba don kuwa Super Falcons ba kanwar lasa ba ce idan aka zo batun kwazo a fagen wasa.