Nottingham Forest ta kori Arsenal wadda ta lashe gasar sau 14 a gasar cin kofin FA na kakar bana bayan da ta yi nasara da 1-0 a yammacin jiya Lahadi.
Kungiyar ta Championship da Mikel Arteta na Arsenal sun yi kunnen doki a hutun rabin lokaci a karshen wasan, ba tare da wani bangare ya samu nasara ba.
Sai dai Lewis Grabban ne ya baiwa ‘yan wasan na gida damar cin kwallo a minti na 83 da fara wasa, inda ya farke kwallon da kwallon da Ryan Yates ya kawo daga wuri Mai nisa, inda suka Yi nasara da 1-0, Wanda hakan ya Basu damar buga wasa da Leicester mai rike da kofin, a zagaye na hudu.
Sakamakon ya nuna cewa an fitar da Arsenal a zagaye na uku na gasar a karo na biyu a cikin shekaru 26 da suka gabata.
Kazalika ko a shekarar 2018 Nottingham Forest din ce ta yi Awon gaba da Arsernal a gasar tun a karo na uku, makamancin wannan.
Masu masaukin baki sun kasance mafi kyawu tun daga farko har zuwa karshen karawar duk da rashin cinkwallon da suka yi.
Sun riga sun yi rashin nasara a wasanni biyu a shekarar 2022 bayan da suka Sami rashin nasara a hannun zakarun Premier Manchester City a wasansu na farko na bana.