Dan wasan tsakiya Shooting Stars na Ibadan , Kelly Kester ba zai buga karawar da kungiyarsa za ta yi da Akwa United a gasar Firimiyar Najeriya a yau a filin wasa na Lekan Salami dake garin Adamasingba ba, saboda rauni.
Tsohon dan wasan tsakiyar Akwa United ya bayyanawa DAILY POST cewa a halin yanzu yana jinyar rauni a gwiwarsa.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
Kester ya kara da cewa zai shafe watanni yana jinya saboda yana fatan dawowa a lokacin kashin karshe na kakar wasan bana.
“Wannan wasa ne da na so in buga saboda na san Akwa United sosai.” Inji Kester.
“Babu jindadi ga rauni (guiwa) da na samu a wasanmu na gida da Bendel Insurance. in ji shi.
A wani labarin kuma, Yan bindiga Sun Yi Ruwan Wuta A Wurin Kamfen Din APC, Mutum 1 Ya Kwanta Dama
Wasu ‘yan bindiga a karshen mako sun kashe mutum daya a wurin yakin neman zabe na jam’iyyar APC a Ebonyi. Kamar yadda The Nayion ta ruwaito.
Matar wani dan jarida a jihar ta tsallake rijiya da baya a yayin harin inda ‘yan bindigar suka harbe wasu.