Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Legas zuwa Kano da Ajaokuta saboda fargabar hare-haren ta’addanci.
Wasu majiyoyi da dama daga hukumar NRC sun shaida wa daya daga cikin ‘yan jaridu cewa ba za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa ba har sai an tabbatar da tsaro a kan hanyar Legas zuwa Kano da tashar jirgin kasa ta Ajaokuta.
An kuma bayyana cewa NRC ta dakatar da ayyuka a tashar Ajaokuta da ke kan hanyar Warri-Itakpe saboda harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa wasu fasinjoji a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN KARIN LABARIN: mun samar da tsarin tattaunawa da ASUU na wuccin gadi
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Legas zuwa Kano ne saboda rashin tsaro da ake fama da shi a jihohin Neja da Kaduna, wadanda su ne hanyoyin jirgin da ke kan hanyar zuwa Kano daga Legas.
Shugaban hukumar ta NRC, Fidet Okhiria, ya tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a tashar Ajaokuta da hanyar Legas zuwa Kano a wata Sanarwa daya fitar ranar Talata.
Da yake magana game da jigilar da suke yi akan hanyar Warri-Itakpe, ya ce, “Ba mu tsayar da ayyuka gaba daya ba, amma abin da muka ce shine zamu dakatar da aikin mu a tashar Ajaokuta.
A cewarsa, baya ga hanyar Abuja zuwa Kaduna, kamfanin ya kuma dakatar da zirga-zirgar hanyar Legas zuwa Kano saboda matsalar tsaro.
Da aka tambaye shi ko akwai wani jirgin kasa da ba ya aiki baya ga titin Abuja zuwa Kaduna, shugaban NRC ya ce, “A’a, ban da Legas zuwa Kano, saboda ayyukan ‘yan fashin da suka shafi hanyar Kaduna ne; kuma an dakatar da shi, (Lagos-Kano) saboda sai mun bi ta Minna da Kaduna idan za mu je Kano.
Don haka dole mu dakatar da shi a yanzu.” inji shi.
A ranar 13 ga Agusta, 2021, gwamnatin tarayya ta dawo da aikin titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.
Manajan shiyyar Arewa na Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya, Mista Ismail Adebiyi ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar 8 ga watan Agusta.
A watan Maris din bana, kamfanin ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Legas zuwa Kano, bayan da aka samu matsala a Jebba, jihar Kwara a watan Fabrairu.
Okhiria, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a kan jiragen kasa, inda ya kara da cewa an tura karin dakaru daga jami’an ‘yan sanda da na Civil Defence domin kare kayayyakin.