NSCDC ta horas da Jami’an ta kan bunƙasa zaman lafiya da Sasanci a Katsina
Hukumar Jami’an Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens (NSCDC) ta shirya taron wayar dakai, da horaswar Jami’an dake faɗin Ƙananan Hukumomi 34 na Jahar Katsina.
A lokacin taron horswar a ranar Juma’a a Katsina, Shugaban bada horon, CSC Abdulkadir Umar yace taron horaswar akan bunƙasa zaman lafiya da magance fadace-fadace nada manufar inganta aikace-aikacen Hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akwai yiwuwar in koma PDP ko NNPP — Inji Ɗan Ƴar’uwar Shugaba Buhari
Umar ya bayyana cewar taron horaswar akan bunƙasa zaman lafiya da magance fadace-fadace na daga cikin makaman da ake amfani dashi wajen yin dubi akan ƙwazon Jami’an daga Hukumar, da kuma Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida dana Kasashen Waje suke yi.
“Taron horaswar yayi dai-dai ne da kudirin Shugaban Hukumar na sake inganta aikace-aikace, da ƙara ƙaimi, da kuma canja mata wani matsaya domin inganta ayyukan Hukumar.
Shalkwatar Hukumar na Ƙasa dake Abuja, ta shirya taron wayar da kai akan Bunƙasa zaman lafiya ta hanyar amfani da Dabarun sasanci a cikin Al’umma.
“Wannan taron horaswa ya kasance wani muhimmin mataki na ganin Jami’an Hukumar suna da masaniya akan yadda zasu Bunƙasa zaman lafiya ba tare da amfani da makamai ba.
“Daga cikin abubuwan da aka tattauna sun ƙunshi hanyoyi da za’a bunƙasa a dukkanin sassan Hukumar daga shalkwatar ta Ƙasa zuwa ga ƙaramin jami’i, a yayin da Jami’an zasu magance manyan matsaloli ta hanyar abinda ya shafi bunkasa zaman lafiya da Dabaru.
Daga cikin lamarin da yake da wahala a bunƙasa zaman lafiya ya kunshi, faɗan Makiyaya da Manoma da rikicin bashi, da matsala ta cikin gida gami da rikicin Fili da Gona.
Ya yi kira ga mahalarta taron dasu haɗa hannu da takwarorin su na Hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance fadace-fadace.
Yace Hukumomin tsaro, da masu riƙe da Sarautun gargajiya, da Shuwagabannin Addinai, da Kungiyoyin cikin Al’umma, dole su tattauna akan abubuwan dake damun Al’umma, tare da inganta zumunci da zaman lafiya.
Kwamandan Hukumar na Jaha Mohammed Sanusi yayi kira ga mahalarta taron dasu yi amfani da dukkanin abubuwan da aka tattauna, tare da bin Dokoki na aiki.
Ya kuma yi marhaba da wannan shiri na Shugaban Hukumar Ahmed Abubakar Audi daya shirya wannan taron karawa juna sani, da kuma inganta horon Jami’an Hukumar.