Kwamanda-Janar na Hukumar Jami’an tsaron Sibil difens Dr Ahmed Audi, yace sun tura jami’ai dubu 20,000 domin gudanar da zaɓen Gwamnan Anambra wanda zai gudanar a ranar Asabar.
Yace tura jami’an nada nufin samar da tsaro akan kai hari ga masu zaɓe, da kuma tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gidauniyar Sanata Uba Sani Ta Tallafawa Wanda Fashewar Tankar Mai Ya Shafa
Dayake jawabi a lokacin ziyarar duba yanayi zuwa Anambra gabanin zaɓe, Audi ya kuma gargaɗi jami’an tsaro akan yin amfani da ƙarfi a lokacin zaɓen.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Hukumar na Ƙasa Olusola Odumosu ya fitar.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwuiwa na Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta da Sauran Masu ruwa da tsaki a lokacin gudanar da zaɓen, yana bada tabbacin cewa zaɓen zai gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba, yana mai bayyana cewa jami’an tsaron zasu yi aiki da sauran Hukumomin tsaro, gami da magance kai hari ga masu zaɓe, da kayyakin gudanar da zabe da Ma’aikatan INEC.