Hukumar lura da jami’o’in Nijeriya, NUC ta fara karbar bayanai wadanda za su tabbatar mata yiwuwar cewa jami’o’in Nijeriya a shirye suke su ci gaba da karatunsu a yayin annobar cutar korona.
Shugaban hukumar, Abubakar Adamu Rasheed shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, a birnin tarayya Abuja a yayin da yake ganawa da ‘yan jarida akan gudummawar da jami’o’i ke bayarwa wajen dakile yaduwar annobar cutar korona a kasarnan.
Dr Suleiman Ramon Yusuf, mataimakin shugaban kumar a bangaren lura da karatuttuka, shi ne ya wakilci shugaban NUC din, inda ya tabbatar da cewa hukumar ta su suna nazarin samar da mafita dangane da rikita-rikitar da yake akwai da kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU dangane da yajin aikin da suke yi da kuma batun bude jami’o’in.
Ya kara da cewa a halin yanzu, NUC na aiki da jami’o’i domin sanin irin shirin da suke da shi da kuma wanda suka tanada na bude jami’o’in. Inda ya ce da zarar an kammala shirye-shirye, jami’o’in da ba sa karkashin ASUU za su iya komawa makaranta.