Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Nuhu Ribadu, ya musanta danganta kowa da Dan bindiga.
Ribadu, jigo ne a jam’iyyar APC, a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Abuja, yayi watsi da wani fai-fan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta cewa, yayi maganganun da ke danganta wasu mutane da ‘yan bindiga a kasar nan.
Ya ce: “An danganta ni da maganganun karya kuma na gani a cikin shafukan sada zumunta da yawa. Koyaya, har yanzu ina samun kira daga mutane a duk faɗin duniya don tabbatarwa da ce wa, ko na yi wannan batu.
“Zan ci gaba da cewa ban taba cewa wasu manyan mutane suna bayan daukar nauyin ‘yan bindiga ba,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Kai hari Ofishin Yan sanda a Adamawa
Ya kuma musanta yin wata hira a cikin rahoton, wanda ba a rubuta shi sosai ba kuma yake yaduwa tun a shekarar 2019.
Yayin da yake yabawa kafafen yada labarai na ainihi saboda rashin zurfafa bincike a cikin rahoton na karya, ya bukaci mutane da kada su dumama fagen siyasa da kalaman batanci da za su haifar da rikici a kasar nan, gabanin zaben shekarar 2023.
“Kisan kare dangi na Rwanda ya fara ne daga labaran karya, kuma ya kai ga asarar rayuka kusan miliyan daya. Haka lamarin ya kasance da Saliyo da Laberiya. Babu wani amfanin hakan ga kowa, ”in ji shi.
Comments 1