Kungiyar yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi ta yi Allah wadai da wani halin da ta alakanta shi da na kare wanfa jami’an yan sanda suka yiwa daya daga cikin yan jaridar jihar.
A ranar Alhamis ne yan sandan suka ci zarafin wani mai daukar hoto na tashar talabijin din AIT mai suna Damina Yusuf yayin da yake bakin aiki a gurin zanga-zangar daliban kwalejin noma na jihar ta Bauchi.
Kungiyar ta ce ba za ta lamunci ganin yadda jami’an yan sanda ke ci gaba da cin zarafin ƴaƴanta ba, don haka dole ne ta ɗauki mataki.
Kungiyar ta faɗa fa kakkausar murya cewa tilas ne rundunar ta biya diyya wa fan jaridar tare da maido masa da duk kayan aikinsa da aka kwace gami da wadanda aka lalata.
Wannan shine karo na biyar a jere cikin shekara guda da jami’an yan sandar ke wannan nummunar aika-aika kan yan jarida, wanda na baya bayan nan shine wanda ya faru kan dan jaridar tashar Talabijin ta kasa NTA Halliru Ahmad.
Tuni kuma NUJ din ta umarci mambobinta da su kauracewa daukar rahotan duk wats hidima da ta shafi rundunar yan sandar jihar nan take.