Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya (NULGE) reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da kin amincewa da kudirin dokar cin gashin kan kananan hukumomi da majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi.
NULGE ta ce kin amincewa da kudirin ya zama koma baya ga ingantacciyar ci gaban jihar da ma kasa baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Ta Dauki Ma’aikatan Lafiya 1,000 Aiki
Majalisar dokokin jihar ta yi la’akari da kudurin a kwanan baya tare da wasu kudirorin da suka samu daga majalisar dokokin kasar amma suka gaza yin aiki yayin da aka zartar da wasu kudirori da dama da suka hada da na ‘yancin cin gashin kai na bangaren shari’a da majalisar dokokin jihar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar NULGE reshen jihar Kaduna, Rayyanu Isyaku Turunku ya fitar a jiya, ya bayyana matakin da majalisar ta dauka a matsayin babban abin takaici domin ya saba wa alkawuran da kungiyar ta dauka.
Ya kara da cewa majalisar zartarwar kungiyar ta kasa za ta sake duba lamarin a lokacin da ya dace sannan ta tashi tsaye.
A wani labarin kuma, Ka Daina Aiki A Matsayin Mai Taimaka Wa Wike, APC Ta Fadawa Makinde
Jam’iyyar APC a jihar Oyo ta tuhumi gwamna Seyi Makinde bisa zargin rashin gudanar da ayyukansa tun bayan hawansa mulki a watan Mayun shekarar 2019.
Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa Makinde abinda yayi bai taka kara ya karya ba duk da cewa jihar na karbar kaso mafi girma fiye da sauran jihohi da dama.