Akalla matasa masu yi wa kasa hidima karkashin shirin NYSC guda dari bakwai da talatin da bakwai (737), daga rukunin B na shekarar 2020 ne suka kamu da cutar COVID-19.
Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na dakile cutar COVID-19, Boss Mustapha ya bayyana hakan a ranar Talata.
A cewar sa, matasan sun kamu da cutar ne daga dukkanin jihohin kasar.
KARANTA WANNAN: Hukumar DSS ba ta fara daukar aiki ba, mutane su yi hattara da ‘yan damfara
“Dangane da batu kan matasa masu yi wa kasa hidima karkashin shirin NYSC, kwamitin PTF ya gudanar da gwajin cutar ga matasa a rukunin B ta hanyar amfani da RDTs,” a cewar sa.
“Daga cikin matasa 35,419 da ke a rukunin B, an samu matasa 731 dauke da wannan cuta da COVID-19, sabanin mutane 108 da aka samu a rukunin A.
“An samu matasan dauke da wannan cuta ne daga kowacce jiha da ke cikin kasar Nigeria”.