Hukumar NYSC wacce keda alhakin kula da shirin bautar kasa da duk matashi da matsayita wanda ya kammala karatun digiri ko HND ta koka matuka akan karuwar masu karatun karya a Najeriya.
Shugaban Hukuma Brigediya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a wani taron horaswa da hukumar ta saba shiryawa kafin daukar sabbin yan bautar kasa na kashi na 3 wanda akafi sani da batch C a turance na shekarar 2019, wanda hukumar ta shirya a Minna babban birnin jahar Neja.
A cewar Shugaban an samu daliban bogi guda 95 a kashi na biyu wato batch B na wannan shekarar.
Bincike ya nuna cewa an samu dalibai 60 daga jamioin cikin gida sannan kuma guda 35 daga jamioinda suke sauran kasashen Afrika ta yamma.
Abin takaicin shine yanda makarantun suka tura mana sunayen daliban bogin ta hanyarda ya kamata, inda sunayen na kunshe cikin jerin dalibai da Majalisar Dattijai da kuma hukumar karatun makarantun wato suka turo mana ta hanyar yanar gizo. Wannan abun damuwa ne matuka, hakan na nuni da sakaci da halin ko in kula da makarantun ke nunawa! Wanda hakan cin amana ne karara A cewarsa Brigediya Janar Shuaibu Ibrahim.
Sannan ya kara da cewa kwanan nan za’a sake diban yan kashi na uku, ina rokar duk wani mai takardar bogi da kar su bata lokacinsu.
Comments 1