Hukumar Kula da Masu yiwa Ƙasa Hidima a ranar Laraba ta nuna damuwarta na rashin kyawawan gine-gine da yanayin da sansanonin su a faɗin Ƙasa.
Hukumar ta ɗora alhakin hakan ga rashin wasu masu ruwa da tsaki na suyi ayyukan su yadda ya kamata musamman a Jahohi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Fidda Gwani: Masu zaɓe zasu sanya layi bayan fastar ɗan takarar da suke so a Ekiti — Badaru
Darkta-Janar na Hukumar Manjo-Janar Shuaibu Ibrahim ya bayyana hakan a lokacin taron NYSC na shekarar 2022 a Abuja.
Taron dai an kirashi ne domin tattaunawa akan yanayin yadda wuraren suke a faɗin ƙasa.
Ibrahim ya bayyana cewar, “duk da irin nasarorin da suka cimmawa, amma shirin horas da matasa masu yiwa ƙasa hidima na fuskantar matsaloli. Wannan ya faru ne sakamakon rashin sauke nauyin da masu ruwa da tsaki suka yi.
Ya bayyana damuwa na ƙarancin sana’o’i ga matasan, tuni yana taɓa nagartar su.