Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya kori Mista Edomwonyi Iduozee Ogiegbaen a matsayin Enogie na Egbaen Siluko a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo.
Korar Ogiegbaen ta zo ne bayan an tsige shi a matsayin babban ko-odinetan fada a kan al’amuran Enigie a watan Janairu, 2023, bisa zargin tawaye, rashin aiki da kuma tayar da zaune tsaye a Enigie fold a Masarautar Benin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Buni Ya Yi Alhinin Mutuwar Mutane 3 Da Wasu 6 Suka Jikkata A Wani Hatsarin Mota
Oba Ewuare ya kuma sanar da nadin kaftin Uwadiae Ohonbamumwen mai ritaya a matsayin Odionwere na Egbaen Siluko.
Tun da farko a jawabinsa ga sarautar Benin, Ohonbamumwen, tsohon Ozukpogieva (dattijo mafi girma na biyu a Egbaen Siluko), ya nisanta kansa daga cin zarafi da aka yi wa Ogiegbaen, wanda ya ce a fili ya ki girmama wasu roko da aka yi masa na ya koma kan matakinsa.
Ya koka da yadda wasu kararrakin da dattawan masarautar suka yi wa Ogiegbaen sun shiga kunnen uwar shegu bayan da ya jagoranci wasu jiga-jigan ‘yan adawa suka shigar da karar gwamnatin Jihar Edo, inda suka bukaci a ba su kundin tsarin mulkin kananan hukumomin Edo ta Kudu a kokarinsu na ballewa daga masarautar Benin.
Ya kuma roki oba da ya nada shugaban gudanarwa a Egbaen Siluko, wanda ya ce shekaru biyar da suka wuce, domin ceto yankin daga rashin bin doka da oda.
A halin da ake ciki, Sarkin Benin ya kuma nada Mista Aimuamwosa Oyemwense Agidi a matsayin Odionwere na Obazuwa Dukedom a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas gabanin nada Enogie na gaba a Obazuwa.
Oba Ewuare II ya ayyana Aimuamwosa a matsayin Odionwere na Obazuwa bayan ya sasanta dattijai a yankin.
Odionwere ya yi alkawarin hada kan al’ummarsa da tabbatar da ci gaba a yankin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ba a kayyade ranar da za a gudanar da bukukuwan nadawa da za a gudanar da bikin na gargajiya ba.
A wani labarin kuma, Jam’iyyar APC Ta Kaddamar Da Daraktoci 22 Na Yakin Neman Zaben Gwamna
Jam’iyyar APC reshen jihar Neja, ta kaddamar da daraktoci 22 cikin 24 na kwamitin yakin neman zaben gwamna Umar Mohammed Bago, gabanin babban zabe mai zuwa a kasar nan.
Bago, a lokacin da yake kaddamar da kwamitin yakin neman zaben a Minna, ya bukaci ‘yan kungiyar da su hada kai ba tare da raba zargi ga juna ba domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a dukkan matakai a jihar.