Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles wato Obafemi Martins ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wuhan Zall dake ƙasar China bayan ya bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Shanghai Shanhua watta itama take a ƙasar ta China wato ƙungiyar ƙwallon ƙafan da Odian Ighalo yake fafata wasansa kafin ya koma Manchester United a matsayin aro.
Martins dai kafin ya bar Shanghai Shanhua ya bugamusu wasanni guda 40 inda ya jefa ƙwallaye 19 sai dai a wasanni guda 4 daya buga a baya-bayannan baijefa ƙwallo ko guda ba.
Ɗan wasan ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Wuhan Zall ne inda ya sanyamusu kwantaragin shekara ɗaya wato zuwa shekarar 2021 kenan daza a shiga nan da watanni uku.
Martins dai a yanzu haka yana da shekaru 35 a duniya inda sa’anninsa tuni suka rataye takalmansu amma shi har yanzu yana fafata wasan ƙwallon ƙafa sosai da sosai kuma kamar bashi da niyyar jingine takalman nasa inda ake zaton cewar zai iya kai shekaru 40 yana buga wasa.