Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yace rancen kudin da ake yi domin tarawa yan baya bashi mai yawa, ta’addanci ne.
Obasanjo ya bayyana haka, a lokacin da yake maida martani akan Shirin Gwamnatin Tarayya na Kara karbo bashi a kasashen waje.
A satin daya gabata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa Majalisar Dattijai wasika data amince ya sake ciwo bashi, na Dala biliyan $4,054,476,863 da euro miliyan €710 ‘kari a cikin tsarin bashin da aka ciwo daga Shekarar 2018 zuwa 2020.
Buhari Ya Isa New York Don Halattar Taron Majalisar Dinkin Duniya
A cikin takardar da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan ya karantawa Majalisar, Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar samun ‘karin kudade domin gudanar da wasu ayyuka masu mahimmanci a Kasar.
Duk da Jami’iyyar APC tayi bayani akan ciwo bashin, amma mutane da dama sun kalubalanci lamarin.
Abun mamaki, Ali Ndume, Sanata a Jami’iyyar APC daga Jahar Borno, yace ya damu matuka akan yadda Majalisun ke rige-rigen amince wa da ciwo basussuka.
Dayake jawabi a gidan talabijin na Channels, Obasanjo yace idan bashin da aka ciwo aka barshi ba’a biya ba, to zaya iya zama matsala a gwamnatoci masu zuwa.
Yace ciwo bashi ba matsala bane, amma amso shi a wuraren da baka da halin biya shine matsalar.
“Idan ka Gina wajen kasuwanci, kuma kaje ka karanto kudi, kuma kana da kashi 50 na kudin ka, kuma ka aro kashi 50, to a cikin shekaru 5, sai ka biya kashi 50 da ka ranto. Wannan shi yafi dace wa kayi. Amma idan kaje ka ranto kudaden da bazaka iya ciyar da kanka da iyalan ka, wannan shine wawancin da zaka yi.”
“Idan kana rance kana tarawa yan baya bashi, to ta’addanci ne. To suwa kake ranto mawa?
“Idan kana ciwo da bashi domin wani aiki to shine makurar abinda bai dace ba. Amma idan kana rancen kudi domin samar da cigaba to zai biya kanshi, Kuma shine abun fahimta. To kenan yaushe ne bashin zai dauki lokaci ya biya kansa?”
Tsohon Shugaban Kasa yace a lokacin wa’adin mulkin sa a Shekarar 1999, Kasar na biyan Dala biliyan $3.5 domin biyan kudaden bashi da yake hauhawa.
Comments 1