Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya musanta zargin cewa yana kokarin kafa sabuwar jam’iyya a ƙasar nan, inda ya ce wadanda suka kirkiri labarin ya kamata su ziyarci asibitin kwakwalwa.
Tsohon shugaban kasar ya ce an kirkiro da labarin da niyyar shafa mishi kashin kaji don haka tilas a guji irin wannan dabi’a.
Ya ce a matsayin na dattijon siyasa yana da ƴancin fitowa don tattaunawa da waɗanda ya ga damar yin hakan.
Obasanjo ya yi wannan kalamai ne a cikin wata sanarwa daga hadiminsa a fuskar yaɗa labarai Kehinde Akinyemi.
Ya ce a yanzu haka jam’iyyar siyasarsa kawai ita ce irin kunci da yan Najeriya ke ciki wanda yake fatan a samu mafita nan gaba kaɗan.