Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a ranar Litinin ya sanya tubalin ginin makarantar yara masu nakasa a garin Igbor dake kusa da Makurdi a jihar Binuwe.
Makarantar wanda ita ce irinta ta farko, Cocin Catholic Diocese dake Makurdi ne zai gina ta.
Rahotanni sun bayyana cewa garin Igbor yana titin Makurdi/Aliade ne kusa da sansanin masu ziyarar kirista dake Ayati wanda shi ne muhallin Cocin Catholic Diocese din.
Obasanjo, a wurin muhallin ya yi takaicin yadda al’umma ta yi watsi da yara masu nakasa duk da kuwa suna da bukatar taimakon al’ummar.
A don haka Obasanjo ya jinjinawa Cocin Catholic din bisa wannan aiki da za su, wanda ya ce tabbas sun tuna da bukatar nakasassaun, inda ya shawarce su da su hada hannu da gwamnati wajen samar da abubuwan bukata da suke nema domin tabbatar da aikin na su.