Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a wata zanga-zangar da ta kai ga lalata bankuna da kuma mutuwar kimanin mutane uku a jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare, ya fitar a ranar Laraba, Obaseki ya yi zargin cewa Oshimohole ya hada ‘yan baranda domin lalata bankuna tare da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar saboda karancin kudin naira.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sabbin Kudin Naira: An Dawo Da Takardun Kudi Da Suka Kai Tiriliyan 2.1 – Buhari
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun yini a kusa da birnin, muna zantawa da masu zanga-zangar, kuma mun gano cewa ya fi gaban ido.
“A wannan mataki, muna kira ga jami’an tsaro da su kamo Adams Oshiomhole domin yi masa tambayoyi da kuma duba yadda ya tafiyar da lamarin, musamman a nan birnin Benin a kwanakin baya. Da gangan ya tada zanga-zangar jama’a.
“Na san mutane za su ga zanga-zangar sakamakon karancin kudin Naira, amma ko da haka ne, ya kamata ‘yan Nijeriya su san ko wace jam’iyyar siyasa ce ke da ruwa da tsaki, domin abin mamaki ne a ce jam’iyyar da ke da alhakin wannan manufar ita ce har yanzu ta tura mutane su lalata allunan tallan jam’iyyar PDP.”
A wani labarin kuma, Dalilin Da Ya Sa Muka Ki Amincewa Da Bukatar Buhari Ta Daina Amfani Da Tsoffin Kudi – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya bayyana cewa jami’an gwamnatin tarayya sun tuntube shi da wasu gwamnonin kan hanyoyin da za su sasanta ba tare da kotu ba kan sabuwar manufar kudin Naira.
Sai dai ya yi watsi da tayin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.