Ofishin babban mai binciken kudi na Tarayya ya tuhumi mahukuntan Majalisar Dokoki ta kasa da Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa bisa zargin kashe Naira Biliyan 9.4 da ba a bayyana ba a cikin kasafin kudin shekarar 2019.
Rahoton ya ce kimanin Naira biliyan 5.5 na irin wannan kashi an baiwa Majalisar Wakilai ne a abu guda biyar da ake nema, Naira biliyan 3.5 da aka bai wa Majalisar a cikin neman tantancewa guda bakwai, yayin da Naira miliyan 307.6 aka ba Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa a cikin tambayoyin dubawa guda biyu.
Abubuwan da ake nema suna kunshe ne a cikin rahoton shekara-shekara na Odita Janar na rashin bin ka’ida da kuma matsalolin da suka shafi rashin bin doka da oda a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya na shekarar da ta kare a ranar 31 ga Disamba, 2019.
Rahoton da aka gabatar wa magatakarda na Majalisar Dokoki ta kasa ya samu sa hannun babban mai binciken kudi na tarayya, Adolphus Agughu.
Rahoton ya ce an bai wa ‘yan majalisar wakilai Naira biliyan 2.5 a matsayin kudin tafiyar da harkokin gudanarwa tsakanin watan Yuli zuwa Disambar 2019 ba tare da wata shaida da ta nuna abin da aka yi amfani da kudaden ba duk da cewa babu ritaya ba.
Har ila yau, an bayar da Naira miliyan 258 ga ma’aikatan majalisar 59, yayin da kuma aka baiwa wasu ma’aikatan biyu Naira miliyan 107.9 domin yin gyara da kuma kula da gidajen da ba a bayyana ba, wanda hakan ya hana gwamnati biyan harajin VAT miliyan 10.7 da aka kayyade idan har majalisar ta amince da hakan an ba da aikin ga yan kwangila.