Wani da ake zargin rikakken mai garkuwa da mutane kuma Dan fashi da makami Sanusi Lauwali, wanda yan sanda suka kama a Bauchi yace, ya kashe akalla mutane biyar a lokacin fadan addini a Jos, Jahar Filato.
Lauwali ya bayyana haka a lokacin da kwamishinan Yan sanda na Jahar Bauchi Sylvester Alabi yayi holen shi a hedikwatar Jahar.
Dan shekaru 27, yace a duk lokacin da akace akwai rikicin addini a Jahar Filato, ogan shi ke bashi bindigu domin kashe kiristoci, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta The Punch ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: An Kama Wata Mata Da Laifin Damfarar ‘Yan Kasuwa Da Katin Gargadi Na Banki Na Karya
Ya kara dacewa, duk da bazai iya nuna irin adadin mutanen daya kashe ba, amma baza suyi ‘kasa da biyar ba.
Yace “bazan iya tuna yawan mutanen dana kashe ba, amma bazasu kai goma ba, bazasu yi kasa da biyar ba.
“Na kashe su ne a lokacin fadan addini a Jahar Filato. Sune wadanda na harbe kuma na kashe.”
A lokacin da aka tambaye shi inda yake samun bindigar da yake amfani da’ita wajen kisan, yace: “Shugaban mu ne ke bani bindigun kamar yadda Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta within Nigeria ta fitar.
Ya kara dacewa, “Ina zama a kauyen Tunga, wajen garin Jos, amma duk lokacin da akace akwai fadace-fadace, zai turamu zuwa wurin domin mu kashe kiristoci.
“Na gudu na koma garina, a Karamar Hukumar Ningi na tsawon shekara daya a halin yanzu, bayan na koma ne suka sanar da Jami’an tsaro wanda suka kama ni, duk da nasan inada laifi na abunda ake tuhuma ta dashi.”
Haka zalika, CP Alabi ya shaidawa Manema Labaru cewa Lauwali, wanda akafi sani da ‘no delay’ Dan Asalin kauyen Gudale a Karamar Hukumar Ningi ta Jahar Bauchi, ya kasance rikakken mai garkuwa da mutane, kuma Dan fashi da makami.
Yace Wanda ake zargin an kamashi ne, a ranar 12 ga watan Satumba na Shekarar 2021, da misalin karfe 5 na yamma ta hanyar bayanan sirri da aka samu.
Alabi ya bayyana cewa akwai yan tawagar sa da suka hada da wani Ali, da Bammi gami da welcome (har yanzu ba’a sunan shi ba).
“Ya tabbatar da amfana da dubu dari 250,000 a matsayin la’adar sa na ta’addancin da suke aikatawa, ga wani wanda suka sace a kauyen Dabar Tsintsiya.
Kwamishinan Yan sandan yace ana cigaba da gudanar da bincike, domin kamo sauran abokanan gudanar da ta’addancin.