By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi dan shekara 32 mai suna Biodun Adebiyi da laifin dukan wani mai sayar da sigari mai shekaru 30 wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa har lahira a kan kudi naira 50.
Kamen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya raba wa manema labarai a Abeokuta.
Oyeyemi a cewar an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifin marigayin, Adamu Abubaka ya kai hedikwatar Idiroko, inda ya bayyana cewa wanda ake zargin yazo shagonsa dake unguwar Ajegunle a Idiroko da misalin karfe 2 na rana domin sayen sigari da dansa, Mukaila Adamu ya halarta.
Ya ci gaba da cewa da misalin karfe 10 na dare wanda ake zargin ya dawo ya bukaci a biya shi N50. Hakan ya haifar da cece-kuce a tsakaninsa da dansa, kuma a cikin ta kaddamar wanda ake zargin ya yi wa dan nasa Mukaila Adamu duka da mari, wanda hakan ya sa dan nasa ya fadi kasa, inda tuni aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Bayan rahoton, DPO, reshen Idiroko, CSP Shadrach Oriloye, ya yi gaggawar kai mutanensa wurin da lamarin ya faru, inda nan take aka cafke wanda ake zargin.
Tuni dai aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da bincike.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa sashin binciken laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gabam kotu.