By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS), reshen jihar Ogun a ranar Talata ta yi kira ga sarakunan gargajiya a jihar Ogun da su rika wayar da kan al’ummarsu kan illolin dake tattare da kai wa jami’an hukumar ta jihar hari.
Kwanturola na yankin, Dera Nnadi shine ya yi wannan kira a ranar Talata a Abeokuta, yayin da yake jawabi ga shugabannin gargajiya a wani bangare na kokarin ganin kwamandan ya kulla alaka da masu ruwa da tsaki da sauran al’ummomin dake cikin rundunar.
Sannan ya yi tsokaci kan mutuwar jami’an hukumar fasa kwairi guda biyu da wasu da ake zargin ‘yan fasa kwauri ne suka kashe a watan Oktoba, 2021.
Nnadi, don haka ya yi kira ga sarakunan gargajiya na Yewaland wadanda yankunansu ke zama tushen masu aikata laifi, hakance tasa hukumar hana fasa kwauri tashi tsaye wajen fuskantar kalubale.
Shugaban hana fasa kwauri tare da jami’an sa sun zagaya zuwa fadar Olu na Ilaro kuma mai mulkin Yewaland, Oba Kehinde Olugbenle, Dakta Adedotun Aremu Gbadebo da kuma Agura na Gbagura, Oba Sabur Babajide Bakre.
Nnadi, wanda ya yi magana a fadar Agura na Gbagura, Abeokuta, Oba Sabur Babajide Bakre, wanda shi kansa babban jami’in hukumar hana fasa kwauri ne mai ritaya, ya bayyana cewa NCS a karkashinsa za ta yaba da hadin kai da fadar da garuruwan suke yi domin shawo kan kalubalen dake fuskantar ayyukan fasa-kwaurin da yake yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.