By Ishaq Dabai
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC reshen jihar Ogun ta koka kan karancin halartar masu karbar katin zabe kashi na farko na aikin rijistar masu kada kuri’a CVR da ke gudana a jihar Ogun.
Sabon Kwamishinan Zabe na Jihar Ogun, Mista Olusegun Agbaje wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar, yace, jihar ta yi rijistar mafi karancin masu jefa kuri’a a Kudu maso Yamma, idan aka kwatanta da jihohin Osun, Ondo da Ekiti.
Da yake bayar da alkaluman wadanda suka yi rijista kawo zuwa yanzu, Agbaje ya ce, mazauna jihar su 46,937 su kayi rajista ta yanar gizo yayin da mutum guda 12,231 ne kawai suka kammala yin rajistar a zahiri.Ya kuma bayyana cewa jihar Osun tana da rijistar masu kada kuri’a guda 63,259, yayin da Ondo take da mutane 20,632 inda kuma mutane 19,128 da suka yi rajista a jihar Ekiti.
Agbaje ya ce, “a karshen kashi na farko na masu yin rijistar ta yanar gizo a ranar 21 ga Satumba 2021, mutane guda 46,937 ne kawai suka yi rajista a yanar gizo tare da kuma mutane guda 12, 231 da suka kammala rajista idan aka kwatanta da jihohin Ondo, Ekiti, da Osun.
”Wadanda shekarunsu suka kai 18 da kuma sama basu yi rajista ba da kuma masu rajistar da suke da matsala yayin tantancewa a lokacin duk wani zaben da ya gabata, tare da PVCs ko yatsun hannun su basa futa wanda na’urar katin zabe baya karba.
“Masu yin katin zabe da masu yin rijista waɗanda ke son gyara bayanan su, kamar sunayen da ba a rubuta su ba, kwanakin haihuwa, da sauransu, basa buƙatar yin rijistar sakamakon suna neman gyara da sauya bayanan su.