Jam’iyyar APC reshen jihar Ogun, ta kammala shirin dakatar da Cif Derin Adebiyi, shugaban jam’iyyar a jihar da tsohon Gwamna Ibikunle Amosun ke marawa baya, kan wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyyar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wasu majiyoyi da dama a sakatariyar jam’iyyar APC sun tabbatar da cewa an gano Adebiyi da wasu ‘yan jam’iyyar masu biyayya ga Amosun sun kafa jerin sunayen wakilan da suka halarci zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC a jihar, kamar yadda jaridar DAILY POST ta rawaito.
Karanta kuma: Jam’iyatar APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbi Da Aka Gudanar A Jihar Ogun
Ku tuna cewa Amosun, Sanata mai wakiltar mazabar Ogun ta tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya sha fama da rikici da tsohon abokinsa, Dapo Abiodun, wanda shine gwamnan jihar mai ci.