By Abbas Yakubu Yaura
Uwargidan gwamnan jihar Ogun, Misis Bamidele Abiodun a ranar Alhamis, ta bayyana cewa dole ne a yi kokarin daukar karin ma’aikatan jinya da unguwarzoma domin rage mace-macen mata masu juna biyu a fadin jihar.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana haka ne a wajen taron da kungiyar ci gaban al’umma da kuma matan Ogun suka shirya kan lafiyar mata da ma’aikatan wanda aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar.Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai don taimakawa wajen inganta harkar kiwon lafiya a yankunan karkara.
A cewarta, akwai bukatar a samar da daidaito ga mata a yankunan karkara dangane da lafiyar mata masu juna biyu.sannan tace,“Ya kamata mu kara himma wajen daukar karin ma’aikatan jinya da unguwarzoma domin rage mace-macen mata masu juna biyu a jihar. Inganta yanayin lafiyar mata masu juna biyu a yankunan karkara a jihar Ogun zai bukaci hadin kan mu baki daya.
Abiodun ta kara da cewa, “Ya kamata mu karfafawa ‘ya’yanmu su je makarantar koyon aikin jinya. In sha Allahu zan yi magana da kwamishiniyar lafiya ta yi wani abu, ita mace ce kuma tana kishin duk wani abu da ya shafi mata, zan kuma yi magana da Gwamna ya yi wani abu akai game da daukar mata aiki.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Kungiyar reshen jihar ta koka kan karancin ma’aikatan jinya a jihar. Kungiyar ta kuma ce akwai ma’aikatan jinya 215 a jihar da ke aiki a cibiyoyin lafiya 448 dake fadin jihar.