Wani direban Tanka ya hallaka mutane biyu, yayin da wasu biyun suka jikkata.
Hakan ta afku ne bayan wani hatsari daya auku akan hanyar Legas zuwa Ibadan a yankin karamar hukumar Sagamu dake jihar Ogun.
Hatsarin dai ya faru ne da misalin karfe 6 na safe, tsakanin mai motar Tanka, da wata Motar Haya kirar Hayis.
Mai magana da yawun hukumar lura da zirga-zirgar ababan hawa a jihar Ogun Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace hatsarin ya afku ne sakamakon shanyewar birki da Tankar tayi.
To sai dai ya ce Direban Tankar tuni ya cika wandansa da Iska saboda gudun me kaje yazo.