By Ishaq Dabai
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu da wasu karin mutane biyu a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 30.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an yi garkuwa da mutanen uku ranar Lahadi da yamma akan hanyar Igbo zuwa Ora zuwa Sokoto dake karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun.
An kuma tattaro cewa wadanda abin ya rutsa da su sun ziyarci abokin su wanda ke zaune a unguwar Rounda a Abeokuta, babban birnin jihar lokacin da aka sace su,wata majiya ta sanar da cewa masu garkuwar sun yi wa mutane uku kwanton bauna a yankin da ake kira Karigo, inda ta kara da cewa mai ciki tana cikin wata na takwas.
A cewar majiyar, makiyayan a ranar Talata sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa tare da neman su biya naira miliyan 10 kowannensu don a sake su.An ce wasu mutane biyu dake cikin tafiya sun tsere lokacin da masu garkuwa da mutanen suka tare su.
“Masu garkuwar ba su kira nan take ba amma sun kira a ranar Talata, inda suka nemi a ba su Naira miliyan 10 a kan duk wanda aka sace a matsayin kudin fansa. Daga cikin su akwai mace mai ciki, wanda a kowanne lokacin zata iya haihuwa”,
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin.Sai dai Oyeyemi ya ce wadanda abin ya rutsa da su sun shirya yin zaman addu’a a dajin a lokacin da aka kama su.
Ya ce, “tun daga wannan ranar, mutanenmu ke kan turbarsu.A zahiri yayin da nake tattaunawa da Jami’in da ke kula da su, har yanzu suna cikin daji a wannan yankin suna kokarin ganin an sako dukkan mutanen ba tare da sun ji rauni ba “.