By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an kama wani da ake zargi dan fashi da makami ne mai suna Biodun Rasheed, wanda rahotanni suka ce ya yi irin shigar kayan fulani masu kiwo a jihar Ogun.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama shi a wani samame da suka yi na fashi da makami a yankin.
Jami’an ‘yan sandan da ke aiki a hedikwatar sashin Kemta a karamar hukumar Odeda sun samu kiran cewa ana aikata lafin fashi da makami a mile 6 kan hanyar Ajebo, Abeokuta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, a ranar Alhamis, ya shaida wa manema labarai cewa, biyo bayan wannan kiran na gaggawar, DPO reshen Kemta, CSP Opebiyi Sunday, ya yi gaggawar tara tawagarsa ta ‘yan sintiri wadanda suka hada da jami’an So Safe Corps da ’yan banga na Najeriya.
“Da ganin jami’an tsaro sai ‘yan fashin suka yi ta kai ruwa rana, amma sai aka kama su da kyar, daya daga cikin su Biodun Rasheed, wanda ke sanye da kayan Fulani makiyaya don boye sunan sa, nan take aka kama shi.
Oyeyemi ya ce wanda ake zargin “a halin yanzu yana taimakawa ‘yan sanda a kokarin da suke yi na cafke sauran ‘yan kungiyar.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.