Wadanda suka saba dokar hana zirga-zirgar babura kasuwanci na Achaba (Okada) a jihar Legas suna fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda fara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar a ranar Juma’a.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Sufuri na Jihar Legas, Dokta Frederic Oladeinde, wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Ikeja. Ya ce kashi na biyu na dokar hana okada a kananan hukumomi hudu da kuma kananan yankunanan shida.
Karanta kuma: Gwamnatin Legas Na Shirin Kafa Hukumar Hana Sana’ar Okada a Jihar
“Muna rokon jama’a da su yi biyayya, saboda duka mahayi da fasinja dukkansu za su yi zaman gidan yari na shekaru uku idan an gurfanar da su,” in ji Oladeinde.
“Za a damke baburansu tare da murkushe su a idon jama’a, daidai da tanadin sashe na 46, karamin sashe na 1, 2 & 3 na dokar sake fasalin harkokin sufuri (TSRL), 2018.
“Muna kira ga jama’a da su hada kai da gwamnatin jihar ta hanyar bin shawarar da aka yanke na yakar aikin okada ya haifar domin hayyacin jihar mu ya dawo.”
A cewar kwamishinan, jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Legas (LASTMA) 200 ne aka tura tare da sauran hukumomin tsaro domin aiwatar da dokar. Ya bayyana cewar karin wa’adin yana kan hanyar da ta dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Legas.
“A matsayinmu na gwamnati, ba za mu bar fasinjojin da abin ya shafa ba a makale ba tare da wata hanya ta sufuri ba, shi ya sa muka samar da hanyoyin da za a bi wajen zirga-zirga.
“Madaidaicin hanyoyin sufurin ya hada da tsarin sufuri na manyan motocin Mile Bus na farko da na karshe, da tsarin BRT, tsarin motocin haya e-hailing na Legas (LAGRIDE), da sauran hanyoyin sufurin da aka amince da su, don gudanar da ayyukansu na yau da kullun.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa Kwamishinan ya kara da cewa, “Shawara da matsayar gwamnati a kan okada a bayyane yake, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kan wannan shawarar, wato don kara karfafa nasarorin da aka samu zuwa yanzu musamman kan raguwar hadurra da aikata laifuka,” in ji kwamishinan.
A watan Agusta gwamnatin jihar ta ayyana dakatar da wasu kananan hukumomi hudu da kananan yankuna shida musamman a Kosofe (Ikosi-Isheri da Agboyi-Ketu LCDAs); Mushin (Odi-Olowo LCDA); Oshodi (Oshodi-Isolo da Ejigbo LCDAs), kuma a cikin Shomolu (Bariga LCDA).
A wani labarin kuma: ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Daliba A Calabar
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Cross River, CP Aminu Alhassan a ranar Alhamis din nan ya tabbatar da sace wata dalibar lauya mai shekaru 24, Miss Dora Effiom daga gidanta da ke lamba 17 a kan titin Joseph Mkpang , a karamar hukumar Calabar ta jihar.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun tafi da yarinyar ne a cikin motar mahaifiyarta mai suna Grey Toyota Corolla, 2010 da misalin karfe 2:00 na ranar Larabar nan.