Kungiyar ci gaban kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta goyi bayan wacce Najeriya ta zaba domin takarar shugabancin hukumar da ke kula da kasuwancin duniya ta World Trade Organization.
Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kasashen Afirka da su goyi bayanta domin hada kan Afirka.
Najeriya ta zabi DR Ngozi Okonji-Iweala, wacce tsohuwar ministar kudi ce domin takarar mukamin.
“Muna kira ga gwamnatocin Afirka, da na sauran duniya da su goyi bayan Dr. Ngozi Okonjo-Iweala,” a cewar shugaban kasar Jamhuriyar Nijar kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS Mahamadou Issoufou a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar.
Duk da cewar an sanya wa sanarwar kwanan watan ranar 19 ga watan Yuni, ba a fitar da ita ba sai a ranar 22 ga watan Yuni.
Mutane da dama na bukatar macce ta shugabanci hukumar tunda abu ne da ba a taba samu ba a can baya.
Magoya bayan Okonjo-Iweala wacce tsohuwar minista ce kuma babbar manajan babban bankin duniya, sun jadadda kwarewarta da kuma yadda ta samo wa Najeriya wasu kudaden da suka kai yawan billiyoyin daloli.
Wannan goyon baya da Okonjo-iweala ke samu ya biyo bayan takaddamar da kasashen Afirka suka dinga samu wajen zabar wanda zai musu wakilci.