Hukumar lafiya ta duniya, WHO a ranar Juma’a ta bai wa tsohuwar ministar kudin Nijeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala mukamin jami’a ta musamman a kwamitin da zai lura da yadda za a yi yaki da cutar Korona, ACT.
Za ta yi aiki ne kafada da kafada da dan kasuwar Birtaniya, Sir Andrew Witty wajen jawo hankalin kasashen duniya domin cimma manufar kawo karshen Korona a duniya.
Shugaban WHO, Dr. Tedros Ghebreyesus, shi ne ya bayyana mukamin na ta da aka ba ta a yayin da kaddamar da shirin na ACT ta webinar a birnin Geneva.
Wannan shiri na ACT shiri ne da WHO suka kaddamar da shi wajen kulla alaka da kasashen duniya domin ganin an kawo ci gaba, tare da samar da kayayyakin yaki da cutar Korona ta hanyar samar da magunguna, kayayyakin gwaji, a duk fadin duniya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan shi ne aiki na hudu a kasashen duniya da aka bai wa Okonjo-Iweala a kasa da wata biyu.