Gwamnatin Jahar Lagos tayi gargaɗin ɗaukar matakin hukunta duk wanda ya karya dokar kariyar cutar Covid-19, da da kuma dokar matafiya ƙasashen waje, kamar yadda Kwamitin Fadar Shugaban Ƙasa akan cutar ya fitar.
Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya ƙara dacewa, Gwamnatin sa ta hanyar kotu na, zasu hukunta duk wanda aka samu yana karya dokar magance cutar Covid-19.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aurata Da Wasu Dalibai Biyu Sun Mutu A Ya Yin Gasar Tseran Motar Daliban Jami’ar Unilorin
A cikin wata sanarwa da Sakataren Ƴan Jaridu na Gwamnan ya sanyawa hannu Gboyega Akosile, tace Gwamantin ta haɗa hannu da Kwamitin Shugaban Ƙasa domin hukunta duk wanda ya ƙi yin rigakafi.
Sanwa-Olu yace “duk wani ɗan ƙasar waje daya karya dokar, to za’a mai dashi. A saboda haka nake roƙon duk wani matafiyi daya yi duk wani gwaji da ake buƙata, a kowane Asibitin da aka amince dashi a Lagos.”
Comments 1