By Ishaq Dabai
Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Ondo tace ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da hada baki wajen yin sata, kutse da mallakar mitoci takwas da aka biya kafin lokacin satar.
Yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi kwamandan jihar Ondo, Hammed Abodunrin ya sake nanatawa a bayyane cewa hukumar tsaro ta farin kaya tana da alhakin kare dukkan muhimman kadarorin kasa da ababen more rayuwa a fadin jihar saboda haka ba za a taɓa kula da irin waɗannan ayyuka masu kaifi ba.
A cikin kalamansa “Biyo bayan aikin da rundunar ta yi, Babban Kwamandan, Ahmed Abubakar Audi, a cikin taron jami’an gudanarwa da masu ruwa da tsaki ya jaddada bukatar sake rubanya kokarinmu na kare dukkan muhimman kadarorin kasa da abubuwan more rayuwa; tare da wannan sashi na hukumar Ondo a shirye take ta kama tare da gurfanar da duk masu laifin. ”
Kwamandan rundunar yace an samu nasarar cafke mutanen ne ta hanyar samun bayanan sirri, don haka Sashen Kula da Kaya da Aiki na rundunar ya shiga aiki tare da cafke babban wanda ake zargi, Osuola Gospel mai shekaru 26, wanda ya fito daga jihar Imo amma a halin yanzu yana zaune a gida mai lamba 4, Ogunyebi Street, Ijapo Extension, Akure.