Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a garin Owo na jihar Ondo.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, 2022, a mahadar Folahami, inda wani kamfanin gine-gine mai suna Craneburg Construction yake.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Motar Mai Ta Tarwatse A Jihar Kwara Ta Kone Direba
Harin na zuwane watanni biyu bayan kisan kiyashin da aka yi a cocin St. Francis Catholic, Owo,dake jihar Ondo wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 38.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan wadanda ke wurin a yayin da lamarin ya afku.
Wata majiyar da ta yi magana a boye ta yi zargin cewa an kuma yi amfani da wasu bama-bamai a yayin harin.
Sai dai har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba har ya zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto amma an ce mutane da dama sun jikkata a harin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutane uku sun samu raunuka a wani harbi da aka yi a garin.
Odunlami ta ce ba za ta iya tabbatar da cewa maharan ‘yan ta’adda ne ko kuma ‘yan bindiga ne kawai ba.
A cewar ta, “An yi harbin ne a kamfanin Craneburg Construction Owo, a halin yanzu ‘yan sanda suna wurin, an kai wadanda abin ya shafa zuwa asibiti kuma suna cikin koshin lafiya.
“Ba za mu iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba a yanzu haka kuma ba za mu iya cewa harin na ‘yan ta’adda ne da suka yi amfani da bama-bamai ba, amma jami’an EOD na rundunar za su je wurin.”
Odunlami ta yi kira ga mazauna garin da kada su firgita domin an shawo kan lamarin.