By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Ondo Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu yayi Allah wadai kan shugabancin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore na tambayar gwamnatin tarayya da majalissar dokoki jihar dasu dakatar da dokar hana kiwo a sarari da gwamnatin jihar ta sanya.
Gwamnan ya fadi hakan ne ta cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin ayyuka na musamman Darkta Doyin Odebowale ya fitar, yace Akeredolu ya bayyana bara zanar da kungiyar take yi a matsayin ba’abune mai yiwuwa ba a halatta musu shi a cikin jama’a.
Sanarwar wacce aka fitar cikin wani ta kaitaccen faifan bidiyo “gwamnatin jihar Ondo tayi kira ga kungiyar makiyay ta Miyyati Allah Kautal Hore inda ya fada ta hanyar sakataren ta Sale Hassan, yace wannan ba dabi’ar su bace, wannan ba al’adarsu bace bayyananniya babu wata shakka da zatasa a bada goyan baya ga masu aikata laifuka.
“Babu kowanne irin kabilanci a zahiri yan asalin wajen, ‘yan siyasa subada dama ga sauran mutane da suka dace a doron kasa ba ‘yan bindiga, da masu fyde da ‘yan fashi ba, ya zama wajibi ga kowacce kungiyar da magoya bayan ta subi doka.