By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, a jiya Asabar, ta tabbatar da sakin gawar marigayi dalibin kwalejin Dowen, Sylvester Oromoni, ga danginsa domin yi masa jana’iza.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Adekunle Ajisebutu, yace an saki gawar ne bayan kammala binciken gawar domin gano musabbabin mutuwar da kuma yanayin mutuwar tasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An kai gawar Sylvester zuwa Legas ne a ranar Litinin daga jihar Delta domin gudanar da cikakken bincike a wani wurin jama’a.
An ce an gudanar da binciken gawar ne a gaban bangarorin biyar, na Iyayen wanda aka kashe, da kuma iyayen daliban da ake zargi da hannu a cikin mutuwar sa, da wakilan makarantar, da ‘yan sandan masu binciken, yayin da wakilai daga ma’aikatar lafiya suka tsaya a matsayin masu wakiltar gwamnatin jihar Legas.
A ranar Laraba ne aka mayar da gawar zuwa Delta inda za a yi jana’izar Sylvester.
Sai dai har yanzu ba a fitar da sakamakon binciken gawar ba yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike.
Ana zargin Sylvester ya mutu ne daga raunukan daya samu a lokacin da wasu abokan aikinsa guda biyar suka kai masa hari da suka so su sanya shi cikin kungiyar asiri.
Sai dai kuma a wani bangare na hanyoyin samun adalcin daya dace ga yaron mai shekaru 12, dangin Oromoni sun bukaci a gudanar da bincike kan mutuwar dalibin.