Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci Najeriya da Cote d’Ivoire da su samar da matakan da suka dace domin dakile safarar bakin haure da ke jefa matasa cikin hadari a kasashe daban-daban.
Osibanjo Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast, a wajen taron kasashen biyu na Najeriya da Cote d’Ivoire karo na biyu, wanda ya jagoranta tare da firaministan Cote d’Ivoire, Patrick Jerome Achi.
Ya kuma ce ci gaba da kulla alaka ta kud-da-kud a fannin tattalin arziki da hada kai, musamman ma a cikin muradin yarjejeniyar hadewar yankin kamar kungiyar ECOWAS da yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA), ta yadda za a samar da karin ayyukan yi ga matasanta, tare da zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Ya kaddamar da Taron Gidauniyar Jagoran Mata da matasan Arewa
Osinbajo, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Laolu Akande ya fitar, ya mika godiyar sa ga shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, da shugaban kasar Cote d’Ivoire, kan abokantakarsa da kyakkyawar alaka da yake da ita wajen karfafa alakar kasashen biyu.
A taron kasashen biyu, sun rattaba hannu kan wasu sabbin yarjejeniyoyin da suka shafi aikin gona; tattalin arzikin dijital; ilimi; al’amuran ofishin jakadanci da shige da fice; da kuma rigakafin fataucin mutane, a tsakanin sauran bangarorin haɗin gwiwa.
A nasa jawabin tun farko, firaministan na Ivory Coast ya ce ya ji dadin yadda kasashen biyu suka amince da sake farfado da hukumar ta kasashen biyu.