Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da jagorantar kasar a yanzu.
Shugaban ya fadi haka ne jim kadan kafin ya tashi daga Abuja domin zuwa Burtaniya da nufin a duba lafiyarsa, kwanaki bayan ya dawo daga kasar Kenya.
Tun da farko dai shugaban ya shirya fara ziyarar ne daga birnin Nairobi na kasar Kenya bayan ya halarci shirin kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) wanda ya cika shekaru 50 a kasar.
Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya ce a ranar 1 ga Maris, daga Kenya, shugaban zai wuce Landan don duba lafiyarsa, wanda zai dauki tsawon makonni biyu.
Sai dai shugaban ya koma Abuja ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1:00 na rana, lamarin da ya janyo cece-kuce.
Amma Malam Garba Shehu, babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya shaida wa Aminiya cewa an dauke tafiyar zuwa ranar Lahadi.
A cewar Adesina, Buhari zai dawo Abuja nan da makonni biyu.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai kafin tashin sa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, Abuja, Buhari ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar mulkin kasar a lokacin da yake kasar waje.
Shugaban ya ce rashin nasa ba zai shafi ayyukan kasar ba domin yana sane da duk wani ci gaba da ke faruwa idan ba ya nan.
Da aka tambaye shi kan yadda kasar za ta yi aiki idan ba ya nan, sai ya ce: “To, ba zan iya cewa ina yin aikin ni kadai ba. Gwamnati tana da cikakkiyar wakilci. Mataimakin shugaban kasa yana can. A tsarin mulki, lokacin da ba na nan, shi ke da iko. Sannan muna da Sakataren Gwamnatin Tarayya sai kuma Shugaban Ma’aikata, don haka babu wata matsala.”