By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya mika takardar neman gafara ga gwamnan jihar Benue Samuel Ortom kan atakin da jami’an tsaron da ke kofar shiga sansanin sojin sama da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue suka dauka.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro da ke aiki da rundunar sojin sama a babbar kofar shiga sansanin sojin sama sun hana gwamna Ortom karbar mataimakin shugaban kasar zuwa jiharsa a ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairu.
Mataimakin shugaban kasar ya yi tattaki ne zuwa garin Wukari na jihar Taraba a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman sojoji na Makurdi da ke Benue domin halartar taron jami’ar tarayya da ke Wukari.
Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati dake Makurdi a safiyar yau, Ortorm ya yi rajistar rashin jin dadinsa bayan an hana shi shiga kofar rundunar sojojin sama, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa tarbar mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. Ya ce ya kamata bangarorin gwamnati su guji hada ayyukan hukuma da siyasa.
A cewar Gwamna Ortom, an gayyace shi ne domin ya tarbi mataimakin shugaban kasar zuwa jihar amma ya yi mamakin yadda wani jami’in sojin saman Najeriya ya yi hakan a madadinsa.
Gwamnan wanda ke matukar sukar gwamnatin Buhari ya yi kira da a dauki matakin ladabtarwa ga jami’an sojin sama a wani abin da ya bayyana a matsayin abin kunya ga ofishin sa.
Yayin da yake rike da wata takarda daga fadar gwamnatin jihar a hukumance ta bukaci ya karbi mataimakin shugaban kasa, Gwamna Ortom ya ce;
“Ba na so in zama wanda ke da shagala, Ina da abubuwa da yawa da zan yi, Yayin da nake magana da ku, ana kewaye da Gwer-West gaba ɗaya, Fulani sun zo suna kona gidaje. Ya kamata in je can amma sai na canza komai don karbar mataimakin shugaban kasa. Ina jin zafi sosai don an ɗauke siyasa fiye da yadda ya kamata.
Babu makiyi na dindindin a siyasa, babu aboki na dindindin. Gobe zan iya zama babban abokin shugaban kasa idan sun zaɓi yin abin da ya dace. Ba ni da wata matsala da Shugaban kasa da Mataimakin Shugaban kasa, kuma duk abubuwan da na fada, an yi su ne don kara darajar ci gaba da daidaita abubuwa. Ban taba zagin Shugaban kasa ko Mataimakin Shugaban kasa ko Gwamnatin Tarayya ba. Amma akwai wasu abubuwa da suke yi da ba daidai ba. “
Sai dai Osinbajo da hukumomin sojin saman Najeriya sun nemi afuwar Gwamna Ortom wanda a karshe ya tarbi mataimakin shugaban kasar a sansanin sojin sama, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hoton gwamnan na tarbar Osinbajo daga baya mai daukar hoto ya saki wa mataimakin shugaban kasa a yammacin ranar.