Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo yace haɗin kan Al’ummomi musamman Hukumomin Duniya, da na yankuna, da Hukumomin Kuɗi zai magance canja Gwamnati da hana juyin Mulki.
Ya bayyana haka da daren Litinin a lokacin da ya karɓi Ministan Ƙasar Ingila a Afirka Vicky Ford, Wanda ya samu wakilcin Wakilin Turai a Najeriya Catriona Laing a Ziyarar da suka kawo a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa, Abuja.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi jawabi akan rashin amincewa ga Shuwagabannin Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin akan juyin Mulki daya faru a Nahiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Ngige ya ɗage taron sa da ASUU zuwa ƙarfe 2 na rana
A cewar sa “akwai maida hankali sosai da ake cigaba dayi a yankin, musamman a yankin Afirka ta Yamma.
“Ina ga dole muyi duba tare da magance wannan juyin Mulki, da kuma wanda suke son karɓe Gwamnati ta kowane hali.
“Ɗaya daga cikin abubuwan da muke yawan tattaunawa a tarukan mu na ECOWAS shine mu nemi goyon baya daga sauran duniya, musamman Ƙungiyoyi irin su UN da EU da kuma wasu Bankuna domin su marawa wannan korar da muke wa ƙasashen da akayi juyin mulki.