By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa jihar Anambra domin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.
Osinbajo, wanda ya isa wurin taron,a Otal din Finotel, Awka, da misalin karfe 10:58 na safe, yanzu haka yana ganawar sirri da ‘ya’yan jam’iyyar APC.
Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Kudu Maso Gabas Sunyi Kiran A Saki Nnamdi Kanu
Daukacin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ne suka hallara domin tarbar mataimakin shugaban kasar.
A halin da ake ciki, an bukaci ‘yan jarida da su fice daga wurin taron don “ba da damar yin ganawar sirri” tare da ‘yan jam’iyyar APC.
Gwamnan jihar Farfesa Chukwuma Soludo ne ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Cargo na Anambra da ke Umueri domin tarbar mataimakin shugaban kasar.
Ziyar ta mataimakin shugaban kasa bata rasa na saba da takarar sa ta neman maye gurbin kujerar shugaba Buhari.
Kazalika ba wannan ne karon farko da mataimakin shugaban kasar ya yi irin wannan tattaunawa da masu ruwa da tsaki ta jam’iyyar APC ba.
Comments 1