Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, SAN, ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari, a taron bukin zagayowar ranar Sojojin Najeriya wato Nigeria Army Day, a Ikeja, jahar Legas.
Wadan da suka karbe shi a taron, sun hada da Mataimakin Gwamnan jihar Lagos Dr. Femi Hamzat da Shugaban rundunar sojoji Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai da kuma wasu manyan shugabannin mulkin kasa da jihohi.