By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Litinin ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
DUBA WANNAN LABARIN: Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Ede Ta Dakatar Da Zaben Kungiyar Dalibai Biyo Bayan Barkewar Tashin Hankali
Osinbajo ya ziyarci jihar ne domin halartar wani taron tattaunawa da kungiyar hadin kan Afrika CoDA wanda ta shirya.
Tattaunawar da aka yi wa lakabi da, ‘Afirka Ta Yamma Ta Tashi Daga Ƙalubalen Ƙarfafa Mulkin Demokraɗiyya’ za ta gudana ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL),dake Abeokuta a ranakun Litinin da Talata.
Jirgin na Osinbajo ya sauka a cikin harabar OOPL da misalin karfe 10:24 na safe.
A tare da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da sauran su, Obasanjo ya tarbe Osinbajo a yayin da suka wuce wurin da aka shirya taron.
Osinbajo wanda ake kyautata zaton zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023, bai bayyana aniyar sa ba duk da bukatar da kungiyoyin siyasa daban-daban suka yi na bayyana kudirin sa.
Ziyarar tasa na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan jam’iyyar APC mai mulki ta kammala babban taronta na kasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa yakin neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya samu karbuwa a dukkanin bangarori inda kungiyoyi daban-daban da magoya bayansa ke kokarin ganin ya zama shugaban kasa.