Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an sojojin Najeriya a ranar Juma’a sun cafke shugaban kungiyar NURTW a karamar hukumar Olorunda ta jihar Osun, Mista Kazeem Oyewale, wanda aka fi sani da Asiri Eniba.
Ko da yake har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka kame shi har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/an-haifi-jarirai-70-a-sansanin-yan-gudun-hijirar-benue-yayin-da-wasu-200-ke-fuskantar-%c6%99aura-sema/
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro daga majiya mai tushe cewa kamun ba zai rasa nasaba da yadda ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar na ranar Asabar ba.
Daya daga cikin majiyar ta ce, Oyewale, wanda kuma dan jam’iyyar APC mai mulki ne, wasu sojoji dauke da bindigogi ne suka kama shi a Tsohon garejin kungiyar NURTW da ke Osogbo, tare da wasu magoya bayansa.
A halin da ake ciki, jam’iyyar PDP reshen jihar Osun, a makonnin da suka gabata, ta zargi jam’iyyar APC da yin amfani da Oyewale da magoya bayansa wajen kai wa ‘ya’yanta hari a jihar a wani bangare na tunkarar zaben.
Amma, da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sand jihar Osun, Misis Yemisi Opalola ta ce ba a yi wa ‘yan sanda bayanin kama Oyewale ba.
A Wani Labarin Kuma Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta hana kungiyar tsaro ta Osun mai suna Amotekun shiga ayyukan samar da tsaro a zaben gwamna da za a yi ranar Asabar.
Umurnin kotun ya kuma umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kada ta yi amfani da rundunar Amotekun a matsayin wani bangare na jami’an da za a tura domin samar da tsaro a zaben.
Umurnin ya gargadi Amotekun da kada ta zama jami’in tsaro ko kuma na ayyukan sa kai a zaben gwamna.
Wani bangare na umarnin ya ce, “An hana wanda ake kara na 1 (INEC) daga neman a tura wanda ake kara na biyu (AMOTEKUN) a matsayin wani bangare na jami’an tsaro da aka tura domin samar da tsaro a zaben gwamnan Osun 2022 har zuwa lokacin da za a tantance asalin sammacin. Wandanda aka shigar da karar.
Da yake magana game da hukuncin kotun, Hashim Abioye ya bayyana cewa, “Da wannan umarni, ya haramtawa hukumar zabe ta INEC yin amfani da Amotekun a matsayin jami’an tsaro da za a tsara domin gudanar da zaben.
“A yayin da nake magana da ku, an yi wa wadanda abin ya shafa, INEC, ‘yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa aiki yadda ya kamata.”