Osun: Adeleke ya buɗe ta a fai-fai kan batun taimakon Ministan Buhari
Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya Musanta batun Jita-jitar dake yawo cewa Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola ya yi mashi aiki tuƙuru a zaɓen da aka kammala na Gwamna.
Idan dai za’a tuna Adeleke da Jam’iyyar PDP a ranar Lahadi an ayyana su a matsayin wanda ya lashe Zaben Gwamnan Jahar Osun, bayan ya doke Gwamna Gboyega Oyetola.
KARANTA WANNAN LABARIN: Borno Ta Sami Bullar Cutar Kyandar Buri Guda Hudu
Akwai Jita-jitar dake yawo cewa Aregbesola, wanda suna da wata rashin fahimta tsakanin sa da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu na daga cikin abinda ya sanya Adeleke ya samu nasara.
Amma da yake jawabi da gidan talabijin na Channels a Daren ranar Litinin, Adeleke yace bi taɓa magana da Aregbesola ba, a lokacin da zaɓen ya ƙara to.
Amma ya tabbatar da cewa wasu makusantan Ministan sun haɗa hannu dashi domin kada Gwamna mai ci a yanzu, wanda shine Ɗan Takarar Jam’iyya mai mulki ta APC.
Yace “banyi aiki da Aregbesola, banma yi magana dashi ba, amma nasan wasu ƴan Jam’iyyar APC da wasu makusantan sa, sun haɗa hannu damu. Bazan iya faɗin cewa ko Aregbesola ne ya buƙaci makusantan sa su goyi bayana ba, ko ba haka ba, domin ban taɓa tattaunawa dashi ba.
Da aka buƙace shi daya yi bayani akan yanda aka gudanar da zaɓen, Adeleke yace “ba abu bane mai sauƙi ka kada Gwamna mai ci a ko’ina a Duniya.