Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sanata Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar PDP murna bayan nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar din nan.
Sakon taya murnan shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina, ya fitar ranar Lahadin nan a Abuja.
Shugaban ya bayyana yakinin cewa bayan kammala zabe, al’ummar Osun sun bayyana ra’ayinsu ta hanyar jefa kuri’a, kuma dole ne a ko da yaushe a mutunta muradin jama’a a tsarin dimokuradiyya.
A cewarsa, yadda zaben ya gudana cikin nasara wata shaida ce da ke nuna balaga da jajircewar dukkan masu ruwa da tsaki – hukumomin zabe, hukumomin tsaro, jam’iyyun siyasa, kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula da kuma masu kada kuri’a, don kara tabbatar da ingancin zabe a tsarin kasar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Buhari ya tabbatar wa al’ummar kasar cewa kudurin gwamnatin nan na yin sahihan zabuka har yanzu bai girgiza ba.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa jami’in zabe na INEC a zaben gwamnan jihar Osun, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe a safiyar Lahadi ya bayyana Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli.
Ya bayyana cewa Adeleke ya samu kuri’u 403,371 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Gwamna Gboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 375,027.
Ogundipe, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Legas, ya ce jam’iyyar (ADP) ta samu kuri’u 10,104 inda ta zo na uku.
Ya kuma ce dan takarar Accord Party ya samu kuri’u 4,515 ya zo na hudu. (NAN)