Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da kashe wata ‘yar kasuwa mai suna Bolaji Akerele, a garin Ile-Ife na jihar Osun bisa zarginsu da yin asiri da ita domin su Sami makudan kudade.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode, ya shaida wa Daily Trust cewa wadanda ake zargin Sunday Olajide, Hammed Semiu, Salawudeen Lukman da Isiaka Salawudeen ne suka hada baki suka kashe matar a Ife, inda suka cire wasu sassan jikinta tare da kai su garin Iwo domin yin Tsafi da zai sa su Sami kudi.
Olokode ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun kashe tare da yin amfani da sassan jikinta wajen shirya bakar sabulu a Iwo da nufin yin arziki bayan sun yi wanka da sabulun.
An ce matar mai sayar da katako ce a Ile-Ife kafin wadanda ake zargin su kashe ta.
CP ya ce wadanda ake zargin sun yaudari matar da cewa suna da katako da ake sayarwa a cikin daji, sai ta bi su cikin daji domin sayen katakon amma a can suka kashe ta.
Ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa sun shake matar ne, inda suka cire sassan jikinta da suke bukata sannan suka jefar da gawarwakinta a daji.
Ya Kara da cewa, jami’an ‘yan sanda na hukumar binciken manyan laifuka ta jihar Osogbo ne suka gano gawar a cikin daji, lamarin da ya kai ga cafke wadanda ake zargin.
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai jaddada cewa za su fuskanci fushin doka.